Thursday 12 February 2026 - 22:11
Ya Ku Al’ummar Iran, Kun Sa Makiya Sun Yanke Kauna / Ya Kamata Dukkanmu Mu Kiyaye Hadin Kan Kasa, Domin Wannan Hadin Kan Yana Da Mutukar Daraja

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a cikin wani sako na talabijin da ya aika a yammacin yau, ya bayyana fitowar miliyoyin mutane a ranar 22 ga watan Bahman a matsayin silar alfahari da karfafa ikon Jamhuriyar Musulunci. Ya bayyana cewa wannan tattaki ya sa makiya yanke kauna daga muradinsu na ganin al’ummar Iran sun mika wuya. Ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka halarci wannan babban yunkuri, tare da kiran kowa da ya kiyaye hadin kan kasa mai mutukar muhimmanci.

A cewar Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Khamenei ya bayyana a cikin sakon nasa zuwa ga al’ummar Iran cewa: "A ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekarar (11/02/2026), kun yi wani babban aiki; kun daukaka kasar Iran, kuma kamar yadda kuka saba, ta hanyar marawa Jamhuriyar Musulunci baya, kun kara karfinta. Makiya wadanda a cikin maganganunsu da shirye-shiryen su suke neman ganin al’ummar Iran sun mika wuya, sun yanke kauna."

Jagoran Juyin Juya Halin ya bayyana lada na wannan babban yunkuri a matsayin samun daukaka, iko, da cikakken ‘yancin kai na kasar Iran, inda ya kara da cewa: "Dukkanmu mu yi kokari mu kiyaye wannan dunkulewar al'umma da hadin kai, domin abu ne mai kima da tsada kwarai da gaske."

Har ila yau, ya jinjina wa al’ummar da suka cika tituna tare da rera taken hadin kai domin nuna asali da karfin halinsu ga makiya, inda ya bayyana cewa: "Ina mika godiyata da gaisuwa ga daukacin al’ummar Iran, da kuma kowane mutum daya da ya halarci wannan babban taro na miliyoyi a fadin kasar."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha